1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kashe mutane biyu a Dalori

Mouhamadou Awal Balarabe
July 26, 2019

A daidai lokacin da aka cika shekaru 10 da kame Mohamed Yusuf da ya haifar da ta'addanci a Najeriya, 'yan Boko Haram sun kutsa cikin sansanin 'yan gudun hijira na Dalori a jihar Borno inda suka kashe mutane akalla biyu.

https://p.dw.com/p/3Mmg0
Nigeria Boko Haram Anschlag
Hoto: picture alliance/AP Photo/J. Ola

Mutane biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da mayakan na Boko Haram suka kai hari a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno SEMA ta ce gwammam 'yan bindiga a kan babura ne suka kutsa cikin sansanin Dalori a ranar Alhamis, inda suka harbe wasu mutane tare da kwace kayan abinci. Dama  Sansanin Dalori da kauyukan da ke kusa sun saba fuskantar hare-hare daga  'yan Boko Haram, inda ko da a cikin watan Janairun 2016, sai da mutane 85 suka mutu lokacin da mayakan suka afka wa kauyen Dalori.

Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da aka cika shekaru goma cif da kame ‘yan Kungiyar da wancan lokaci ake kiransu da 'yan Yusufiyya da kuma jagoransu Mohamed Yusuf. Wannan matakin ne ya haifar da rikicin Boko Haram wanda ya bazu zuwa wasu jihohin Najeriya da ma kasashen makwabta kamar Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar.