1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta zama gagara-badau a Najeriya

June 6, 2014

Jaridun Jamus a wannan mako sun maida hankalinsu musamman kan halin da Najeriya take ciki sakamakon aiyukan tarzoma na kungiyar Boko Haram

https://p.dw.com/p/1CDyC
Nigeria Protest Boko Haram Entführung 26.5.2014
Hoto: picture-alliance/AP

Jaridar Die Tageszeitung ta duba zargin nan ne dake cewa wasu manyan janarorin sojan Najeriya suna taimakawa yan kungiyar Boko Haram. Jaridar ta ce lokacin shari'a a kotun soja, manyan hafsoshin an same su da laifin baiwa yan mkungiyar ta Boko Haram makamai. An dai dade ba'a sami wani yanayi inda jita-jita tayi yawa a kasar ta Najeriya kamar a wannan lokaci ba. Tun da yan Boko Haram suka sace yan mata kusan 300 daga garin Chibok a arewa maso gabashin kasar kusan watanni biyu da suka wuce, ake ta rade-radi a game da dangantakar dake akwai, tsakanin yan kungiyar ta Boko Haram da manyan hafsoshin sojan Najeriya. A yanzu kuma, jaridar Leadership tace an gurfanar da manyan janarori har 15 gaban kotu, wadanda aka same su da laifin taimakawa yan tarzoman dake ci gaba da kisan jama'a.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhi ne a wannanm ako kan batun zanga-zangar masu neman gwamnati ta dauki matakin dawo da yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace. Saboda labarin cewar gwamnati tayi kokarin hana ci gaba da wannan zanga-zanga a Abuja, jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce gamnatin Najeriya tana kokarin rufe bakunan masu adawa da ita ne kawai. Abin dake gudana kasar kuwa, inji jaridar, bai wuce kasawar wannan gwamnati ta Najeriya ba. A makon jiya, aka sami dauki ba dadi tsakanin yan zanga-zangar dake nemn gwamnati ta dawo da yan matan da aka sace da kuma wata kungiyar da gwamnatin ta hada, take kuma goyon bayanta. jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce a bisa lura da karuwar suka da yake sha a ciki da wajen Najeriya, shugaba Goodluck Jonathan jawabi yake tayi da basu da wata makama, ciki har da kama yaki gadan-gadan da yan Boko Haram har sai an ga bayansu.

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta maida hankalinta ne a kan zaben shugaban kasa da aka yi a Malawi, inda ta ce bayan kokarin shigar da tantama a sakamakon zaben, shugaba mai barin gado, Joyce Banda ta amince da kayen da tasha daga abokin takara, kuma sabon shugaba Peter Mutharika. Jaridar tace tun a ranar Asabar Mutharika, masanin fannin shari'a kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar aka rantsar dashi kan mukamin shugaban kasa, bayan da ya lshe kashi 36 cikin dari na kuri'un da aka kada, yayin da Joyce Banda ta sami abin da bai wuce kashi 20 cikin dari ba.

Kasar Sudan ta kudu ta dauki hankali a wannan mako, musmaman sakamakon rashin zaman lafiya tun da ta sami mukin kanta kusan shekaru uku da suka wuce. A game da haka, jaridar Süddeutsche Zeitung tace wakliliyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya, Hilde Johnson ala tilas za ta fice daga kasar, tun kafin ta kammala aikin da aka dora alhakinsa a kanta. Johnson a watan Yuli na shekara ta 2011 Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya nada ta wakiliyarsa ta musamman a Sudan Ta Kudu, kuma jagorar rundunr tabbatar da zamanlafiya a wannan yanki. To amma ya zuwa yanzu ta kasa samun damar bada gudummuwa a kokarin kyautata matsayin mazauna kasar ta Sudn Ta Kudu,.

Hilde Johnson Leiterin UNMISS-Friedensmission Südsudan
Hoto: Charles Atiki/AFP/Getty Images

A karshe jaridar Tagesspiegel ta duba batun yan gudun hijira dake ci gaba da kwararowa zuwa Turi daga Afirka, tare da asarar rayukan da dama daga cikinsu kan hanyar hakan. Jaridar tace ranar Asabar da ta wuce ne jami'an tsaron tekun a Italiya suka ceto yan gudun hijira 3300 daga teku. Hakan ya snya a watanni biyar na farko a wannan shekara, yan gudun hijira kimanin dubu 43 ne aka ceto daga teku kan hanyar su ta shiga Italiya da Turai. Wannan adadi, inji jaridar ya wuce yawan da aka samu a sghekarar da ta wuce gaba daya.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Suleiman Babayo