1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bore a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango

Lateefa Mustpaha Ja'afarDecember 26, 2014

Matasan sun lalata kadarorin gwamnati da dama a Kwango sakamakon zarginta da suke yi da rashin daukan matakai hana hadarurrukan kwale-kwale a kogin Kwango.

https://p.dw.com/p/1EARs
Kongo Bootsunglück
Hoto: picture-alliance/dpa

matasa sun yi bore a Jamhuriyar Dimokaradiyyar KWango bayan da suka zargi mahukuntan kasar da yin sanadiyyar mutuwar mutane akallah 30 sakamakon hadarin da wani kwale-kwale ya yi. Wani babban jami'in gwamnati ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na DPA cewa matasan sun bankawa gine-ginen gwamnati wuta biyo bayan hadarin kwale-kwalen da ya afku a kogin Kwangon yayin da ya nutse a yankin Isangi a kan hanyarsa daga Kisangani. Kawo yanzu dai an samu nasarar ceto sama da mutane 100 da hadarin ya rutsa da su a kogin na Kwango yayin da ake ci gaba da yin binvike. Mahukuntan kasar ta Kwango dai sun ce gwamnati ba ta da hannu a hadarin kwale-kwalen ko kadan.

dpa fbu sit mga