1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutum biyu cikin zanga-zanga a Chadi

Abdoulrazak Garba Babani AH
April 27, 2021

Akalla mutane guda biyu suka mutu a cikin zanga-zangar a birnin Ndjamena da kuma kudancin Chadin domin nuna kin amincewa da mulkin gwamnatin rikon kwarya ta soji.

https://p.dw.com/p/3sdzl
Tschad Demos gegen Übergangsmilitärrat
Hoto: Blaise Dariustone/DW

'Yan sanda a birnin  N'Djamena na Kasar Chadi sun yi amfani da kulake da kuma hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ta barke a kasar. Masu zanga-zangar sun karade titunan birnin inda suke ambaton lafazin "Wakit Tama" wato lokaci ya yi. Da sanyin safiyar yau Talata (27-04-21) ce aka jiyo hayaniyar dubban matasa a kan titunan suna nuna kin amincewa da matakin da majalisar sojojin kasar ta dauka wanda kuma ke samun goyon bayan Faransa na nadin Muhammat Idris Deby a matsayin shugaban kasar sa'oi kalilan bayan rasuwar mahaifinsa. Yan adawa da kungiyoyi masu zaman kansu ne suka kira jerin gwanon da ya haddasa asarar rayukan mutane biyu. Tun dai da yammacin jiya ne mahukuntan Chadin suka haramta zanga-zangar. Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi Allah wadai da tashin hankalin da zanga-zangar ta haddasa yayin da yake karbar bakuncin shugaban Jamhuriyar Demukkaradiyyar Congo kuma shugaban kungiyar tarayyar Afirka Felix Tshisekedi.