1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren Yukren ya kai ga hallakar mutane 67

February 20, 2014

Har yanzu dai tsugunne ba ta ƙare ba a Yukren inda rikicin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kuma har adadin waɗanda suka rasa rayukansu ke ƙaruwa

https://p.dw.com/p/1BD2m
Kiew Proteste 20.02.2014
Hoto: Louisa Gouliamaki/AFP/Getty Images

Ana ƙiyasin cewa mutane 67 ne suka hallaka a ƙasar Yukren tun bayan da masu zanga-zanga suka fara karawa da 'yan sanda ranar talata. Jami'an kiwon lafiya da 'yan adawa sun ce gawawwaki 67 da bakwai aka kai ɗakin gawa a yau alhamis, a yayin da gidan talabijin na ƙasar ya gwado wasu hotuna masu tayar da hankali.

A yanzu haka dai shugaba Victor Yanukovich da masu adawa da manufofin gwamnatinsa waɗanda kuma ke neman shugaban ya yi murabus na kokuwar saita alƙiblar ƙasar, inda al'ummar ta mutane milliyan 46 ta rabu kusan gida biyu masu sha'awan bin manufofin Turai da masu sha'awar na Rasha.

To sai dai a ganawar da shugaban ya yi da ministocin harkokin wajen Jamus da Faransa da Poland na ba shawarar amfani da taswirar hanya mai matakala uku wajen sulhunta wannan rikici.

Wannan shiri ya tanadi samar da gwamatin riƙon ƙwarya, da sauye-sauye a kundin tsarin mulkin ƙasa kafin a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan Majalisar dokoki.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar