1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan ka'idojin yarjejeniyar Brexit

Mohammad Nasiru Awal
August 21, 2019

Sabon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya fada wa Angela Merkel ta Jamus cewa suna bukatar wata yarjejeniya amma dole EU ta yi sassauci.

https://p.dw.com/p/3OIEa
Berlin, Angela Merkel trifft Boris Johnson
Hoto: Reuters/F. Bensch

FM Birtaniya Boris Johnson da a yammacin ranar Laraba ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin ya ce kasar Birtaniya ba za ta iya amincewa da ka'aidojin da aka gindaya game da ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai EU ba wato Brexit.

Mista Jonhson ya ce ka'idojin za su rarraba kan Birtaniya ne za kuma su tilast awa kasar zama cikin yarjeniyoyin kasuwanci da EU ba tare da Birtaniyar ta samu wani 'yanci a kan batutuwan ba.

A dai nata bangare shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi alkawarin tattauna abin da ta kira mafita ta hakika dangane da batun kan iyakar Ireland, batun da ke zama babban tsaiko na cimma matsaya game da ficewar Birtaniyar daga kungiyar EU. Merkel ta ce ba za a sake bude wata tattaunawa dangane da yarjejeniyar ficewar ta Brexit ba.