1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Borno: Hari kan motocin gwamna

Ahmed Salisu
February 13, 2019

Gwamnan jihar Borno Kashim Shetima ya tsallake rijiya ta baya, bayan da mayakan Boko Haram su ka yi wa tawagar yakin neman zaben sa kwanton bauna a tsakanin garuruwan Ngala da Dikwa a kan iyakar Najeriya da Kamaru.

https://p.dw.com/p/3DLCG
Kashim Shettima Gouverneur Bono Nigeria
Hoto: DW/U. Shehu

Wakilinmu da ke Maiduguri Al-Amin Suleiman Muhammad ya rawaito cewar ana bayyana fargabar mutane da dama sun mutu wasu kuma sun bace ba a ji duriyar su ba. Da almurun jiya ne dai mayakan na Boko Haram suka afkawa tawagar yakin neman zaben bayan da motar gwamnan ta wuce inda su ka raba tawagar biyu su ka bude wuta kan motocin da ke baya kamar yadda wasu shaidun gani da ido su ka bayyana.

Rahotanni dai sun nuna cewa gwamnan ya tsira daga wannan harin. Ya zuwa babu wani jawabi da ya fito daga gwamnatin jihar ko kuma jami'an tsaro kan wannan hari wanda ke zuwa kwanaki kalilan kafin gudanar da zaben kasa baki daya wanda gwamnan ya ke takararar kujerar majalisar dattawa.