1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci Turkiya da ta bude kan iyakokinta

Kamaluddeen SaniFebruary 9, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasar Turkiya da ta bude kan iyakokinta ga dubban 'yan gudun hijirar Siriya wadanda ke sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da kasar.

https://p.dw.com/p/1HsJy
UNHCR William Spindler
Hoto: UNHCR/G. Gordon

Wani jami'in likitocin kungiyar na gari na kowa wato Doctors without Borders Ahmad Muhammad wanda ya tabbatar wa manema labarai hakan, ya kuma ce, yanzu haka babu isassun guraren da 'yan gudun hijirar zasu iya kwanciya da mafi yawancin basu da kayan sawa a yayin da ake tsaka da tsananin sanyi.

William Spindler mai magana da yawun hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya cewa yake.

Turkiya ta bar wani adadin mutane da ke ragaita a fili, a yayin da aka hana wasu ketarawa kan iyaka. A don haka muna kira ga Turkiya da ta bude kan iyakokinta ga dukkanin fararen hular Siriya wadanda ke tserewa masifu tare da neman tallafin kasa da kasa.

Majalisar dinkin duniya dai tace sama da mutane dubu 31 da suka hada da mata da kanan yara sun arce daga birnin Aleppo, inda suke kwanciya a sansanonin da ke bude domin gujewa yakin Siriya.