1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari da Atiku na neman hanyoyin nasara a 2019

Uwais Abubakar Idris MAB
October 8, 2018

Fitar da 'yan takarar neman shugaban kasa da manyan jam'iyyu biyu na PDP da APC suka yi a Najeriya ya nuna fafatawar da za’a yi a 2019, abin da ka iya sauya yakin neman zabe a kokuwar kaiwa ga samun shugabancin kasar.

https://p.dw.com/p/36AnL
Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Hoto: Atiku Media Office

Nasarar da tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ta ‘yan adawa ya samu, bayan da ya kayar da mutane 11 da suka yi takara, ya nuna cewar shi ne ke kalubalantar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki. Wannan ya bude sabon babi a guguwar siyasar da ke kadawa, domin kar-ta- san- kar a tsakanin mutanen guda biyu.

Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja ya bayyana hasashensa ga irin fafatawar da za'a yi, inda ya ce " Za'a yi fafatawa mai zafin gaske ganin cewar Atiku Abubakar hamshakin dan siyasa ne da kuma wanda yake yi wa adawa shugaban kasa da ke rike da madafun iko."     

Karikatur von Abdulkareem Baba Aminu - Nigeria APC Krise
Hoto: DW/Abdulkareem Baba Aminu

Alamu na nuna cewar za'a kai ga kartar kasa a tsakanin jam'iyyun biyu a kokari na kaiwa ga madafun iko, duk da rashin dama ta amfani da bangaranci ko addini, Abin da ya sanya Dr Usman Mohammed masanin kimiyyar siyasa a Abuja ya ce ya kamata a yi taka tsantsan.

Bayanai na nuna cewar manyan 'yan takara da Atiku Abubakar ya samu nasara a kansu irin su gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya koma don karbar tikitin gwamnan a PDP, yayin da Sanata Rabiu Musa kwankwaso da Bukola Saraki suka koma don takarar Sanata a mazabansu na Kwara da Kano. Amma ga Isa Tafida Mafindi kwararen dan siyasa ya ce 'yan takara neman shugabancin Najeriyar fa sun san juna.

Al'ummar Najeriya na cike da fata ta samun sauyi a wannan takara da za'a fafata a tsakanin mutanen biyu da kowa ke jin shi kwararre a fagen siyasar Najeriyar.