1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya lashe zaben Najeriya na 2019

Yusuf Bala Nayaya
February 27, 2019

A yayin yakin neman zabe dai Buhari ya sha jaddada neman goyon baya na al'ummar Najeriya su sake ba shi dama don ya dora a yaki da cin hanci da rashawa da matsalar tsaro da farfado da tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3E9BK
Nigeria, Abuja: Präsident Muhammadu Buhari begrüßt seine Unterstützer
Hoto: Reuters/B. Omoboriowo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu a kasar da ke zama babba a nahiyar Afirka. Shugaban dai ya samu wannan nasara ce a wannan Laraba da ke zama ta bawa ranar samu, bayan kuwa tun da fari ya sha alwashi na samun nasara ko da aka tambaye shi ko zai taya abokin hamayya murna idan ya fadi zabe?

A yayin yakin neman zabe dai Buhari ya sha jadda neman goyon baya na al'ummar Najeriya su sake ba shi dama don ya dora a yaki da cin hanci da rashawa da matsalar tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar da ya ga garari a shekarun baya-bayan nan.

Buhari dai na jam'iyyar APC da kusan kuri'u miliyan hudu ne ya kada abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP wanda ke zama babban attajiri kuma tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya, duk kuwa da irin alkawura da ya yi a yakin neman zabe na "farfado da Najeriya ta ci gaba da aiki."