1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya yi alkawarin ceto 'yan matan Cibok a taron MDD

Gazali Abdou TasawaSeptember 29, 2015

Zauren taron Majalissar Dinkin Duniyar dai ya kece da tabi a lokacin da shugaban Najeriyar ke furta wadannan kalamai.

https://p.dw.com/p/1Gf4g
Nigeria Muhammadu Buhari Präsident Rede vor der UN Vollversammlung
Hoto: picture alliance/ZUMA Press

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauki alkawari a jiya Litanin a gaban taron Majalissar Dinkin Duniya cewa zai ceto 'yan matan nan 200 'yan makarantar Cibok da Kungiyar Boko Haram ta sace, dama yin nasara a kan kungiyar ita kanta nan ba da jimawa ba. Zauren taron Majalissar Dinkin Duniyar dai ya kece da tabi a lokacin da shugaban Najeriyar ke furta wadannan kalamai.

Shugaba Buhari ya shaida wa taron Majalissar Dinkin Duniyar cewa gwamnatinsa ta kaddamar da wani tsari mai karko da zai bata damar samun nasara a kan kungiyar ta Boko Haram wacce a cewarsa tuni sojin Najriyar suka shiga farautar 'ya'yanta har a guraren buyarsu inda suka yi nasarar hallaka ko kama wasu daga cikin shugabanninta tare da ceto daruruwan mutanen da kungiyar ta yi garkuwa da su.

Wannan dai shi ne karo na farko da Shugaba Buhari ke halartar taron koli na Majalissar Dinkin Duniyar tun bayan da ya dare karagar milkin kasar ta Najeriya ranar 14 ga watan Aprilun wannan shekara.