1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar gwamnatin Najeriya ta tsaurara matakan tsaro

February 18, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadan hare haren baya-bayannan a kan wasu kauyukan kudancin jihar Borno da aka danganta da kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1BBCG
Hoto: picture-alliance/AP

Kakakin kwamissionar hukumar kare hakkin bil'adama ta majalisar da ke birnin Geneva Ravina Shamdasani, ta bayyana takaicin hukumar dangane da hare haren na karshen mako da ya yi sanadiyyar rayukan fararen hula sama da 100. Acewarta wannan babbar matsala ce da ke bukatar matakai na gaggawa a bangaren gwamnatin Najeriya na kare rayuka da kayayyakin al'ummar da ke yankunan da aka fi afka wa da hari, kana ta gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda ke da alhakin kai harin.

Jihohi uku da ke yankin arewa maso gabashin tarayyar Najeriya dai sun kasance cikin dokar ta baci na wani lokaci, inda aka dauki karin matakan tsaro sakamakon irin barazanar da jihohin ke fuskanta, musamman ma jihar Borno, inda aka fuskanci hare hare a 'yan kwanakin nan. An dai yi asarar rayuka da kayayyaki, a yayin da kawo yanzu dubban daruruwan mutane ke cigaba da tserewa daga matsugunnensu.

Nigeria Kampf gegen Boko Haram Islamisten
Hoto: picture-alliance/AP

Sai dai manazarta da kungiyon kare hakkin bil'adama na ci gaba da yin tsokaci dangane da manufar sabon salon wadannan hare-hare da ake ci gaba da dangantawa da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram. A cewar Mausi Segun da ke nazari kan lamuran Najeriya a kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa ta Human Rights Watch, harin na da nasaba ne da razana al'ummomin da ke zaune a wadannan kauyuka...

Ta ce " ko wane manufa wannan kungiya take neman cimma, akwai dai batun ta korar mutanen wadannan kauyuka daga matsugunnensu, kuma hakan ya kasance da kauyuka sama da 40, da aka kai wa irin wannan hari tun daga farkon wannan shekara".

Kwararru ta fannin tsaro na ganin cewar akwai abunda ke gudana fiye da wanda idanu ke gani kuma kunne ke ji adangane da wadannan hare hare, kamar yadda Dr Abdullahi Wase masani kan sha'anin tsaro ya nunar....

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama dai sun yi amanar cewar, hare haren basu da nasaba da addini ko kabilanci kamar yadda ake zato, inda Mausi Segun ta yi karin haske da cewar.

Nigeria Kampf gegen Boko Haram Islamisten
Hoto: Getty Images/AFP

" Abun da na gani a hare haren bayannan shi ne, yankunan kudancin da suke kai hari a Borno, yanki ne da ke zama mabuyan 'yan Boko Haram, wani misali shi ne, a hare haren da suka a Konduga, sun kone masallatai da wasu wuraren musulumci, don haka babu wanda ya san manufarsu".

A kan haka kwararru kan tsaro a tarayyar Najeriya ke ci gaba da kira ga jama'a da su yi hattarasu kuma lura, domin za'a iya daukar kayan tsaron kasar, a bawa wasu bara gurbi wadanda za su raunana kasa, saboda dalilan siyasa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh