1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar karfafa tsaro a jihar Filato

Abdul-raheem Hassan | Abdullahi Maidawa Kurgwi
October 17, 2017

Al’ummar yankin Irigwe da ke karamar hukumar Bassa a jihar Filato, sun bukaci shugaban Najeriya Mohammdu Buhari da ya dauki matakan gaggawa don kawar da wani abin da suka kira kisan kare dangi da ake neman yi musu.

https://p.dw.com/p/2lzWn
Nigeria Sicherheitskräfte Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP

Wannan kira da al'ummar ta yi dai na kunshe ne cikin wani taron manema labarai da ta kira bayan harin da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 30 a ranakun Lahadi da Litinin, inda shugaban kungiyar raya ci gaba al'ummar ta Irigwe ta kasa bakidaya Sunday Abdu, ya ce a tsakanin mako guda an kashe mutane fiye da 40 akasarin mata da yara da kuma tsoffi.

Suma a nasu bangaren shugabanin kungiyar Miyyetti Allah ta jihar Filato, sun yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa mazauna kauyukan karamar Bassa kuma sun ensanta kansu daga harin.

Nigeria Unruhen Flüchtlinge bei Jos
Hoto: AP

To sai dai kuma wasu na zargin sakaci daga bangaren gwamnatin jihar wajen daukan matakan dakile rikicin, zargin da mashawarcin gwamnan Filato kan ayyukan watsa labarai Dang Jang, yace ba'ayi wa gwamnatin adalci ba.

Masharhanta dai sun lura yakamata gwamnatin jiha ta tashi haikkan wajen magance lamarin wannan matsala ta hare-hare, tun kafin abin ya zarce hankali. Tun ranar Litinin gwamnatin jihar Filato ta ayyana dokar hana zirga-zirga a karamar hukumar Bassa daga karfe shida na yamma zuwa karsfe shida na safe.