1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar karin haske kan batan Khashoggi

Ahmed Salisu
October 14, 2018

Jamus da Birtaniya da Faransa sun ce ya zama wajibi Saudiyya ta yi wa duniya cikakken bayani game da inda dan jaridar kasar Jamal Khashoggi ya ke wanda ya bace bayan da ya shigar ofishin jakadancin Saudiyya a Turkiyya.

https://p.dw.com/p/36XCs
Verschwinden des prominenten saudischen Journalisten Jamal Khashoggi
Hoto: picture-alliance/AA/O. Coban

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fidda a wannan Lahadin, kasashen uku suka ce ya zama dole a bayyana wanda ke da hannu wajen bacewar Khashoggi tare da daukar matakai na ladabtarwa.

Kasashen suka ce duniya ba za ta zuba idanu ta kallo ana yi wa 'yan jarida da 'yancin na fadin albarkacin baki karen-tsaye ba, wannan ne ma ya sanya suka ce suna goyon bayan gudanar da binciken hadin gwiwa da Saudiyya da Turkiyya din ke yi kan bacewar dan jaridar.

Turkiyya dai ta ce ta na zaton an kashe Jamal Khashoggi ne bayan da ya shiga ofishin jakadancin kasar tasa, zargin da Saudiyya din ta musanta.