1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN bukaci kotu ta saki Julian Assange

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 1, 2021

Kwanaki kalilan gabanin yanke hukuncin iza keyar dan jaridar nan Julian Assange zuwa Amirka, kungiyar 'Yan Jaridu na Gari na Kowa, ta yi kira da a saki wanda ya samar da kamfanin kwarmato na Wikileaks nan take.

https://p.dw.com/p/3nRkg
DW Dokumentationen WikiLeaks - Staatsfeind Julian Assange
Julian Assange wanda ya samar da kamfanin kwarmata bayanai na WikileaksHoto: NDR

Acewar manajan kungiyar ta 'Yan Jaridu na Gari na Kowa, zargin da Amirka ke yi wa Assange na da alaka da siyasa ne kawai. Amirka dai na son bayar da misali ne wajen yankewa dan jaridar hukunci. A ranar Litinin mai zuwa hudu ga wannan wata na Janairu da muke ciki ne dai, wata kotu a birnin London na kasar Birtaniya za ta yanke hukuncin mika shi zuwa Amirkan.