1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bukatar sake tsarin kula da kangararru

November 11, 2019

A wani mataki na kare hakkin masu fama da tabin hankali da kangararru a Najeriya, kungiyar Human Right Watch ta nemi gwamnatin Najeriya da ta haramta dauri cikin mari da duk wani nau'in cin zarafi a gidajen kangararun.

https://p.dw.com/p/3Spks
Die Bettel-Schüler aus Nordnigeria
Hoto: DW

Cikin wani rahoton da ta fitar da a wannan Litinin, kungiyar ta Human Right Watch ta ce ana cin zarafin dubban kangararrun kuma ana daure su cikin mari a gidajen kula da kangararun dabam-dabam da ke tarrayar Najeriya. Ana bukatar agaza wa masu fuskantar matsalar ta tabin hankali ba wai cin zarafinsu ko garkame su ba kamar yadda yake faruwa a asibitoci, da gidajen kula da kangarraru na gwamnatin da ma na addinan kasar guda biyu a fada ta rahoton da ya nuna hotunan bidiyon wasu kangararrun da suka ce ana cin zarafin nasu.

 

Senegal Talibes
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/S. Gil Miranda

Cikin gidaje 28 da masu bincike na kungiyar suka kai ga ziyarta a wasu jihohin kasar takwas a tsakanin watan Agusta da na Satumba a bana dai kuma a fada ta rahoton, 27 na bin wannan hanya ta azabtarwa a kokari na neman warkar da kangararrun. Abun kuma da rahoton ya ce ya saba da ka'ida da ma 'yancin kangararrun na samun kulawar da ta dace.
Aniete Ewang dai na zaman mai bincike ta kungiyar a Tarrayar Najeriyar da kuma ta ce kungiyar tana neman haramta daure kangararrun a ko'ina cikin kasar:

"Muna kira ga hukumomi da a cikin gaggawa su haramta daure kangararru a mari ko sarka ko dai a wuraren kula da kangararru na gwamnati ko kuma na gargajiya. Kuma muna neman gwamnatin da ta gudanar da kamfen din waye kan jama'a domin kara wayar da kai kan hakkin na kangarraru da tabbabu, musamman ma a wurare na kulawar al'ada da ma a tsakanin al'umma na gari. Kowa na da 'yancin neman waraka ta kowace hanya. Kowane wuri na kula da tabbabu da kangarraru na daukar cewar yana yin daidai a kan hanyoyin da yake bi, a saboda haka ya zama wajibi gwamnati ta sa dokokin kula da yadda suke tafi da harkokinsu domin ganin ana mutunta masu newan waraka. Haka kuma ya kamata gwamnatin ta ba da damar samar da asibitoci na gwamnati masu saukin samu da kuma arha ta yadda duk mai bukata ta lafiyar na iya samu”.

 

BG 400 Jahre Sklavenhandel Westafrika
Hoto: Reuters/L. Gnago

Tarrayar Najeriyar dake da al'umma kusan miliyan 200 dai na da kasa da gidajen kula da kangararrun 300, adadin kuma da ya yi kasa kwarai da gaske ga kasar da har ila yau ke fuskantar annoba ta miyagun kwayoyi a tsakani na matasa.
Dr Auwal Sani Salihu dai na zaman shugaban sashen kula da masu matsalar ta tabin hankali a asibitin Malam Aminu Kano da ke Kano, kuma a fadarsa tuni kimmiya ta wuce da sanin amfani da marin a kokari na neman waraka ga tabbabun. Har ya zuwa yanzu dai kasar ta Najeriya na tafiya ne bisa wata dokar Turawan mulkin mallaka wajen tafi da harkoki na tabbabu da kangarraru na kasar.Abun kuma da ake ta'allakawa da ruwa da tsaki da yaduwa da ma ayyuka na kafofin kula da lafiyar al'adar.