1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar sauyi a alakar Turai da Afirka

Yusuf Bala Nayaya
May 2, 2017

Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus Sigmar Gabriel ya bayyana cewa akwai bukatar kawo sauyi a alakar da ke tsakanin kasashen nahiyar Afirka da na nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/2cFKl
Bundesaussenminister Sigmar Gabriel l SPD trifft Moussa Faki Mahamat
Hoto: Imago

Gabriel ya bayyana hakan ne  birnin Addis Ababa a lokacin da ya kai ziyara kasar Habasha, yyin wata ziyara aiki da ya kaikasar jim kadan bayan da ya baro Somaliya, inda ya ce ya zama dole kasashen Turai su hada kansu tare da yin magana da murya guda idan a kan batu na tsare-tsarensu a kasashen Afirka, wanda ya ce a yanzu akwai tsare-tsare mabanbanta da kasashen ke yi kuma bakinsu ya rabu yana mai cewa:

"Mafi yawa kasashen na bin son zuciyarsu ne, su kare manufofinsu kawai a Afirka. Wasu lokutan abin kan zama bibiya irin ta ayyukan lokacin Turawan mulkin mallaka."

Minista Gabriel ya kuma ziyarci shelkwatar AU, inda ya gana da Moussa Faki Mahamat sabon shugaban hukumar da bakinsu ya zo daya kan adawa da kafa sansanoni na 'yan gudun hijira a arewacin Afirka, matakin da suka ce ba zai magance batun kwararar 'yan gudun hijira ba. Ya dai ce dole shugabannin na Afirka su zama masu adalci, ta yadda idan an ba da tallafi  zai rinka kai wa ga wadanda suka dace su samu. Ya kuma yi kira na samar da sauyi a siyasar kasar ta Habasha da ke karkashin dokar ta baci bayan zanga-zangar 'yan adawa.