1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukukuwan Kirismeti cikin talauci a Jamus

December 24, 2013

Wani rukuni na Jamusawa na gudanar da bikin Kirismeti cikin kunci sakamakon rashin kudin da za su saya wa 'ya'yansu kyaututtuka da kuma sauran kayayyakin masarufi da ake bukata.

https://p.dw.com/p/1AgRE
Bildergalerie Deutschland Weihnachtsfest
Hoto: picture-alliance/dpa

Yaran Jamusawa miliyan daya da dubu 500 ne ba za su samu kyaututukan Kirismeti ba a wannan shekara ta 2013. Ba don komai ba, sai don iyayensu ba su da kudin da za su yi hidimar gida da shi har kuma su shirya wannan bikin yadda ya kamata. A maimakon haka ma dai tallafin da suke samu daga gwamnati bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da tsadar rayuwa da ake fuskanta a wannan kasa.

Ko da a jihar Baden-Württenberg da ya fi kowane arziki a Jamus, kashi daya bisa goma na mazaunanta na rayuwa hannu baka hannu kwarya a wannan lokaci na Kirismeti. A wasu jihohi na kasar ma dai ciki har da Bremen, adadin Jamusawa da ke fama da talauci ya nika inda kashi daya bisa hudu na al'umma ke cin karo da wannan matsala. Ko da shi ma Christopher Butterwegge, wanda ya rubuta wani littafi mai taken "Talauci a kasa mai da arziki", sai da ya nuna wajibcin rage gibin da ke akwai tsakanin 'yan Rabbana ka wadatamu da kuma masu gida rana idan ana so komai ya daidaita.

Hartz IV-Empfängerin Manuela Ceraceanu
Manuela Ceraceanu na daga cikin Jamusawa matalautaHoto: DW/C. Ignatzi

"Idan 'yan siyasa da alhaki ya rataya musu a wuya ba su daura damarar yakar talauci bil hakki da gaskiya ba, lallai ba za a rabu da Bukar ba. Abin nufi a nan shi ne, za a iya samun yawaitar fashi da makami, da kuma safarar miyagun kwayoyi da za ta iya jefa kasar cikin wani mawuyacin hali."

Maria Ceraceanu na daga cikin Jamusawan da suka samu kansu a cikin mawuyacin hali sakamakon karancin kudin shiga. A baya dai ta dogara da shagonta wajen samun kudin da ta ke bukata domin kula da 'ya'ya da kuma dangi. Amma a yanzu a wannan lokaci na Kirismeti ba ta kai labari ba saboda tallafi da take samu daga hukuma ba ya biya mata daukancin bukatunta. A cewar Horst-Dieter Tontarski babban jami'i a wata kungiyar agaji da ke birnin Bonn wannan yanayin ba karamin tasiri ya ke yi a rayuwar yau da kullum ba.

"Idan pensho ya karu da kashi 0,25 cikin 100, to kudin haya da kuma na wuta da internet da sauransu, su ma sai su na hawan goron zabi. A wannan yanayi idan aka ce talauci na karuwa, ai ba abin mamaki ba ne."

Tuni dai ita wannan Kungiyar agaji da ta kware a raba abinci a nan birnin Bonn ta dukufa domin samar wa mutane dubu uku abinci a wannan mako na shagulgulan kirisimeti. Hasali ma dai tana rabawa duk mutanen da ba su da karfi, dan abin da ba a rasa ba, kama daga alawa zuwa gawaha da ma dai sauran kayayyakin.

Yayin da a daya hannun kuma kungiyar ta raba wa yara tufafi da sauran kaya wasan yara irin na zamani. A cewar Manuela Ceraceanu ba abin da za a ce wa kungiyar ta Bonn, illa Allah san barka.

Hartz IV-Empfängerin Manuela Ceraceanu
Abinci bila adadin wata kungiya ta ke rabawa a Kirismeti a JamusHoto: DW/C. Ignatzi

"Dole ne in yi magana tsakanin da Allah. Idan da a ce babu wannan kungiyar ta Bonn, to da lallai na tsinci kaina cikin wani mawuyacin hali. Sai dai idan mutane sun tallafamin daga bisani."

Ire-iren wadannan Jamusawa dai na gudanar da shagulgulan kirisimeti ne ba tare da walwala ba. Maimakon haka ma dai sallar za ta iya wucewa ta barsu da gammon bashi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai