1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Wadatar abinci

Matakin bunkasa noma a Najeriya

June 14, 2023

Gwamnatin jihar Borno da ke Najeriya ta tashi tsaye domin magance barazanar karancin abinci da yunwa da Bankin duniya gami da hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya su ka yi hasashen.

https://p.dw.com/p/4SZRb
Najeriya I Manomi
Manomi a NajeriyaHoto: Fati Abubakar/AFP

Jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya na daga cikin jihohin da ake fargabar za a samu karancin abinci kamar yadda rahotannin Bankin duniya da majalisar dinkin duniya su ka bayyana. Bisa wannan ne gwamnatin jihar Borno ta dauki matakin shawa kan matsalar da noma ke fusknata a jihar wacce ke fafutukar farfadowa daga amtsalolin tsaro da su ka gurgunta harkokin rayuwa da na tattalin arzikin Kasa na wannan yankin.

Karin Bayani: Kara neman hanyoyin yaki da Boko Haram

Creek forest along Bauchi
Arewacin NajeriyaHoto: DW

Daga cikin matakai da gwamnatin ta dauka a baya baya nan shi ne na samr da kayayyakin noma don karfafawa manoma musamman wadan su ka koma garuruwan don yin noma shi ne na raba Taraktocin noma da kuma takin zamani. Gwamnatin dai ta ce ganin mutane sun koma garuruwan su tare akwai bukatar a samar mu su da tallafi da zai ba su damar yin noma domin magance barazanar yunwa da aka yi hasashen za a iya samu.

Da ma dai bayan samun saukin matsalolin tsaro na rashin tsaro da ake ganin ya hana manoma zuwa gonakin su rashin kayan noma na zamani na daga cikin abubuwan da ake ganin su na hana samun abinci daga noman da ake yi. Sai fai Farfesa Abba Gambo kwararre shehin malamin a fannin horar da ayyukan gona na jami'ar Maiduguri ya ce baya ga wadan Taraktoci ya kamata kuma gwamnati ta samar da iri na zamani.

Kungiyoyin manoma sun ce matakin da gwamnatin jihar Borno ta dauka su ne ake nema sauran gwamnatoci su dauka domin magance matsalolin tsadar abinci da ake fama da shi a wannan lokaci kamar da Hon Muhammad Magaji sakataren Kungiyoyin manom ta Kasa wato AFAN ya bayyana. Masu ruwa da tsaki a harkokin noma da samar da abinci dai sun fatan tallafin kayan noma zai isa ga manoman da aka nufa da kuma fatan su ma za su yi amfani da su ta hanyar da ta dace, maimakon sayar da su ga ‘yan kasuwa kamar yadda aka saba gani a baya.