1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasar arzikin Afirka cikin ayyukan tarzoma

May 9, 2014

Tabarbarewar tsaro musamman a tarayyar Najeriya da ma a wasu kasashen Afirka na barazana ga makomar nahiyar a fannin samun bunkasar tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/1BxLR
World Economic Forum Abuja Ma Nigeria 08.05.2014
Hoto: Reuters

Mahalarta taron tattalin arzikin duniya a kan Afirka a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya sun yi ta tattaunawa tare da tabka mahawara game da sha'anin tsaro da kuma ta'addanci fiye da batun bunkasar tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka. Tabarbarewar tsaro musamman a tarayyar Najeriya da ma a wasu kasashen Afirka na barazana ga makomar nahiyar a fannin samun bunkasar tattalin arziki.

Sace 'yan mata fiye da 200 a arewa maso gabacin Najeriya da hare-haren ta'addanci da kungiyar nan ta Boko Haram ke yi su ne suka mamaye zauren taron tattalin arzikin kasashen Afirkar a Abuja. Donald Kaberuka shugaban Bankin raya kasashen Afirka ya yi tuni da shekaru gommai na 1990 lokacin da mutane da yawa suka shiga halin ni 'yasu sakamakon yake-yake, masifofi da kuma ta'addanci a wasu kasashen Afirka.

"Kasancewarmu a Najeriya a wannan lokaci wani kwakkwaran sako ne cewa ta'addanci ba zai yi nasara ba. Sace 'yan mata na nufin abu guda biyu, ta'addanci da kuma hari a kan 'yancin 'yan matan na samun ilimi."

Jawabi game da hobbasa

Da ma tun farkon bude taron shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mika godiyarsa ga mahalarta taron inda ya bayyana zuwansu da wani yunkuri na yaki da ta'addanci.

Biola Alabi Medienberaterin aus Nigeria
Bola AlabiHoto: DW/ T. Mösch

Asali dai masu shirya taron sun so mayar da hankali ne a kan bunkasar tattalin arzikin Afirka, kuma nahiyar za ta iya tinkarar jerin kalubalen da ke gabanta. A lokacin da take amsa tambaya game da sha'anin tsaro a Najeriya ministar kudin kasar Ngozi Okonjo-Iweala cewa ta yi.

"Ko shakka babu batun tsaro yana da muhimmanci ga ci gaban kasa. Amma a hirar da na yi da masu zuba jari na gano cewa suna kallon Afirka ne na lokaci mai tsawo. Wannan abin sha'awa ne. Sun ga irin alfanun da ke cikinta. Ba sa yi mata kallo na gajeren lokaci da kasada ta gejeren lokaci. Da yawa daga cikinsu cewa suke sun yi wa Afirka shigar sojan badakkare wato sai Baba ta gani."

Ita kuwa Biola Alabi 'yar jarida a Najeriya yaba wa ta yi da irin tsage gaskiya da takwarorin aikinta a Najeriya ke yi.

"Dole a yaba da aikin da 'yan jaridun Najeriya da Afirka ke yi na bin diddigin labaran da suke bayarwa da kuma kwarewar aikin jarida da suke nunawa. Wani abin da muke gani kuma shi ne yadda jama'a ke ba da ta su gudunamawa bisa manufa."

Nigeria Goodluck Jonathan empfängt Li Keqiang
Goodluck Jonathan da Li KeqiangHoto: AFP/Getty Images

Dangantakar Afirka da China

Baya ga damuwa game da tabarbarewar tsaro a nahiyar ta Afirka, wani batun da ya dauki hankali shi ne dangantakar Afirka da kasar China, wadda Firaministan kasar Li Keqiang ya kasance shugaba daya da ba na Afirka ba da ya halarci taron. Yayi amfani da wannan dama wajen yabawa da bunkasar da Afirka ke samu kana ya yi alkawarin tallafa wa ayyukan samar da ababan more rayuwa a wannan nahiya.

Sai dai wani abin damuwa shi ne bunkasar tattalin arziki ba ta tafiya daidai da yawan guraben aikin yi da ake samu. Saboda haka ne hanshakin dan kasuwar nan na Najeriya Aliko Dangote ya kuduri aniyar kawo sauyi.

Weltwirtschaftsforum in Abuja (Nigeria)
Aliko Dangote a tsakiyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

"Babban kalubalen da muke fuskanta yanzu shi ne wasu daga cikin 'yan Afirka sun gwammace su fita da kudinsu waje maimakon zuba jari a Afirka. Yin haka yana karya guiwar 'yan kasuwa. A matsayin dan Afirka dole ne ka zuba jari a nahiyar don karfafa guiwar na waje su shigo nahiyar."

Abu mafi muhimminci kamar yadda masana suka nunar shi ne bankunan Afirka su kara bude kofofinsu ga kanana da matsakaitan kamfanonin Afirka don su ne suka fi kusa da talaka.

Mawallafa: Thomas Mösch / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe