1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Inganta sana'ar noman tumatir a Katsina

March 26, 2019

Kasuwar tumatir ta karamar hukumar Dan Ja a Jihar Katsinan Najeriya kasuwa ce da aka kafa a wani mataki na magance asarar da manoman tumatirin yankin ke yi a lokacin da suke safararsa zuwa kudancin kasar domin sayarwa.

https://p.dw.com/p/3FfsG
Gemüse
Hoto: DW/T. Shahzad

Wannan ce ta sanya 'yan kasuwan suka fito da fasahar yanka tumatirin da suka noma da kuma busar da shi nan take. Hakan ya taimaka wajen rage dunbun asarar da suke yi na danyen tumatirin a lokacin jigilar isa da shi a kasuwannin kudancin kasar. Shugaban kasuwar tumatirin ta garin Dan Ja Malam Idriss Umar ya yi karin bayani:

"A shekarun baya kowane daga cikin manoman tumatirin wannan yanki namu na loda shi ne a danyensa a motoci ya kai a kasuwannin kudancin kasar domin sayarwa. To amma a kwana a tashi kasuwar ta cushe inda ta kai mafiyawancinmu muna yin asara. Amma a yanzu da muka fito da fasahar yanka shi da kuma busar da shi kafin sayarwa, mun rage asarar da muka saba yi domin idan ya bushe ko ba mu samu muka sayar da shi da wuri ba, mukan aje shi tsawon lokaci ba tare da ya bace ba."

Sai dai duk da wannan mataki da manoman karamar hukumar ta Dan Ja suka dauka dan rage asarar da suke cin karo da ita a harakokin kasuwancinsu na tumatiti, manoman sun sake fuskantar wani kalubalen na daban da ya zo masu kusan ba zata a cewar Malam Dahiru Muhammad daya daga cikin masu sana'ar sayar da tumaririn:

Nordnigeria, Tomaten trocknen in der Sonne in Katsina State
Hoto: DW/Z. Umar

"A sakamakon ruwan sama mai yawa da aka yi wanda ya zo mana ba tare da mun akara ba, an tafka asarar ta kwanduna kimanin 400 na busasshen tumatiri wanda ruwa ya lalata kusan baki dayansa. Jama'a da dama sun yi asara domin ko kadan ba a samu aka yi amfani da shi ba. Dan haka muna bukatar taimako daga gwamnati."

Gwamnatin jihar Katsina dai ta soma yanzu daukar matakai da nufin taimaka wa wadannan manoman tumatir ta yadda za su fi cin moriyar sana'ar tasu kamar dai yadda Dakta Abba Yakubu Abdulahi mai bai wa gwamnan Jihar Katsina shawara a harakokin noma da kiwo ya bayyana.

"Akwai shahararren kamfanin nan mai suna Gino wnda jama'a da dama sun san shi. Mun yi magana da su za su zo su kafa kamfani na sarrafa tumatir wanda a lissafin da muka yi zai fi na Dan Gotte girma. Kafa wannan kamfanin zai bai wa illahirin manoman tumatirin jihar damar sayar da tumatirinsu a cikin sauki da farashi mai kyau. Kuma ko baya ga kamfanin na Gino akwai kuma wasu Indiyawa da suma suke son su zo su kafa kamfanin sarrafa tumatirin a nan. Dan haka za mu iya cewa ba da jimawa ba manoman tumatir na jihar Katsina, kakarsu za ta yanke saka. 

Nordnigeria, Tomaten trocknen in der Sonne in Katsina State
Hoto: DW/Z. Umar

Koma dai mi ake ciki duk da matsalolin da ke tattare da wannan sana'a ta noman tumatiri, manoman karamar hukumar Dan Ja ba su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da habbaka wannan sana'a tasu tare da wadatar da kasuwannin jihar ta Katsina da ma na kudancin kasar da wannan haja tasu.