1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso na fuskantar rikicin siyasa

Mouhamadou Awal BalarabeApril 6, 2015

Jam'iyyar CDP ta Blaise Compaore na Burkina Faso ta soki lamarin majalisar rikon kwarya da yunkurin mayar da 'ya'yanta saniyar ware a zaben watan Oktoba mai zuwa

https://p.dw.com/p/1F3KF
Hoto: picture alliance/AP Photo/R. Blackwell

Jam'iyyar da hambararren shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore ya kafa ta bayyana cewa za ta yi tsayuwar daka, don ganin cewa majalisar wucin gadi ba ta kada kuri'ar amincewa da daftarin doka da zai mayar da 'ya'yanta saniyar ware a zabe mai zuwa ba. 'Yan majalisa na jam'iyyun adawa da kuma kungiyoyin farar hula ne suka shigar da daftarin, da zai bayar da damar yi wa dokar zaben Burkina Faso gyaran fuska, inda suka bukaci a zabe mai zuwa, da yin gefe da daukacin mambobin gwamnatin Compaore da kuma wadanda suka goyi bayan yunkurinsa na yin tazarce.

Sai dai kuma jam'iyyar CDP ta Blaise Compaore ba ta da karfin fada a ji a wannan majalisa ta wucin gadi saboda 'yan majalisu 10 cikin 100 take da su, yayin da bangaren da ya shigar da daftarin ke da kashi 55 daga cikin 100 na kujerun majalisar. Tuni dai kungiyoyin farar hula da ke dasawa da tsohon shugaban Compaore suka yi kira da a gudanar da zanga-zanga a ranar Talata mai zuwa, don yin Allah wadai da matakin da majalisar Burkina Faso ke shirin dauka na mayar da wasu 'ya'yan kasar saniyar ware.