1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon kawance tsakanin Burkina Faso da Mali

February 2, 2023

Friministan Burkina Faso ya yi wa gwamnatin sojan kasar Mali tayi na su kafa gungun kasashe biyu don dawo da tsaro a kasashensu

https://p.dw.com/p/4N1dX
Infografik Putsche in ECOWAS Staaten seit 2020 FR
Taswirar kasashen Burkina Faso da Mali

Tayin na zuwa ne a daidai lokacin da kashashen biyu suka raba gari da Faransa bayan korar dakarunta dake jibge a Mali da Burkina Faso.

Firaiministan na Burkina Faso Apollinaire Kyélem de Tambela ya mika wannan bukata ce yayin da ya kai ziyarar kwanaki biyu a kasar Mali inda ya ce kasashen biyu na iya hada karfinsu guri daya cikin mutumta dokokin ko wace kasa don dawo da tsaro a yankinsu.

Ko baya ga harkar tsaro Firaiministan na Burkina Faso na kyautata fatan ganin kasarsa da Mali sun kula hulda mai karfi a fannin bunkasa albarkatun karkashin kasa da noma da kiwo da Allah ya huwace masu, abin da a fadar sa zai taikawa wa kasashen biyu da ake gani tamkar saniyar ware wajen dogaro da kansu ta ku dakile talauci.