1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina ta tsayar da wa'adin rikon kwarya

November 6, 2014

'Yan siyasa da 'yan farar hula da sojojin Burkina Faso sun amince a gudanar da rikon kwarya na shekara guda. sai dai har yanzu ba a san wanda zai yi rikon kwaryar ba.

https://p.dw.com/p/1DiA2
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Rikon kwaryar shekara guda zai bayar da damar shirya zaben 'yan majalisa da kuma na shugaban kasa a watan Nowamba na shekara ta 2015 a Burkina Faso. Wannan dai ya na kunshe ne cikin sanarwar da aka cimma tsakanin sojoji da 'yan siyasa da kuma kungiyoyin farar hula a birnin Ouagadougou, bisa shi shiga tsakanin shugabannin uku na yankin yammacin Afirka ciki har da Goodluck Jonathan na tarayyar Najeriya.

Sai dai kuma sanarwar ba ta bayyana wanda zai jagorancin gwamnatin rikon kwarya ba. Amma kuma shugaban ECOWAS ko CEDEAO John Mahama na Ghana ya ce ya yi imanin cewar nan ba da jimawa ba za a kafa wannan gwamnati.

Tun a ranar Jumma'a da ta gabata ne guguwar neman sauyi ta yi awon gaba da kujerar mulkin Blaise Compaore, wanda ya samu mafaka a kasar Côte d 'Ivoire. Daga bisani ne sojojin Burkina Faso suka kakkage madafun iko tare da yin alkawarin mayar da mulkin hannun fara hula cikin wani takaitaccen lokaci.

Mawalafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman