1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush ya sanya hannu kan dokar kara matsawa gwamnatin Sudan lamba

December 31, 2007
https://p.dw.com/p/CiZh

Shugaba Bush na Amurka ya sanya hannu kan wata doka da ta amince da ƙara matsawa gwamnatin Sudan lamba a fannin tattalin arziki sakamakon abinda ke faruwa a lardin Darfur. Bush yace gwamnatinsa zata ci gaba a ƙoƙarin da take yi na ganin an samu ci gaba mai ma’ana a lardin Darfur ta hanyar kafa takunkumi kan gwamnatin Sudan da kuma a fannin diplomasiya tare da bada goyon baya ga aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya a Darfur. Dokar dai tana mai bada shawara ne ga hukumomin Amurka da kuma masu saka jari masu zaman kansu da janye daga saka jari a kanfanoni dake hulɗa da Sudan.