1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cafke shugaban al-Qa'ida a Pakistan

December 12, 2014

Mahukuntan kasar pakistan sun ba da sanarwar cafke wani mutum da suka bayyana da daya daga cikin manyan kwamandojin sabuwar kungiyar al-Qa'ida ta kudancin Asiya.

https://p.dw.com/p/1E3GH
Hoto: DW/A. Ghani Kakar

Jami'an 'yan sandan kasar Pakistan sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan Jumma'a cewa sun cafke Shahid Usman, da ke cikin shekarunsa na 30 da haihuwa tare da wasu mutane hudu a birnin Karachi, sun kuma samesu da muggan makamai ciki harda abubuwa masu fashewa da nauyinsu ya kai kimanin kilo 10. A watan Satumbar da ya gabata dai sabuwar kungiyar al-Qa'idan reshen kudancin Asiya da ke da shalkwata a wani yanki na kasar Indiya, ta yi kokarin yin fashin jirgin sojojin ruwa na Pakistan kwanaki kalilan bayan da ta bayyana wanzuwarta. 'Yan sandan na Pakistan sun ce Usman shine shugaban sabuwar kungiyar al-Qa'idan reshen birnin Karachi. A ranar hudu ga watan Satumbar da ya gabata ne dai kungiyar al-Qa'ida ta bayyana kafa sabon reshenta a yankin kudancin Asiya, inda kuma shugabanta Ayman al-Zawahiri ya dauki alkawarin kaddamar da ya ki a yankin na kudancin Asiya da ke da al'ummar Musulmi sama da miliyan 400.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu