1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan kudurin dokar man fetir a Najeriya

Uwais Abubakar Idris/PAWMay 12, 2015

Majalisar wakilan Najeriya ta gaza fara muhawara kan kudurin da ake gani zai sauya fasalin tsarin man fetir din kasar domin wasu na ganin za'a yi wa wani bangaren kasar sakiyar da ba ruwa ne

https://p.dw.com/p/1FOsI
Symbolbild Ausfall der Ölpreise
Hoto: picture-alliance/dpa

To ja in ja kana da kudurin dokar sake fasalin sashin man fetir din Najeriyar ke fsukanta wanda tun 2012 aka fara aiki a kansa ba tare da kaiwa ga amincewa da dokar ba saboda sabani da ma rarrabuwar kawunan da ake fuskanta a tsakanin yan majalisar Najeriyar, da ke dagewa a kan yadda za'a tsara su wa keda iko da arzikin man fetir din.

Österreich Wien 166. OPEC Konferenz
Ministan man fetir Diezani Kogbeni Alison-MaduekeHoto: picture-alliance/dpa/H. Pfarrhofer

Wa ke da iko da arzikin man fetir din?

Majalisar wakilan Najeriyar da ta tsara fara muhawara a kan dokar a talata ta gaza yin hakan saboda abinda wasu ‘yan majalisar suka kira kaucewa a yi masu sakiyar da babu ruwa a kan wannan batu, wanda sannu a hankali ke kara daukan hankalin al'ummar kasar. Hon Shuaibu Gwanda Gobir dan majalisar wakialn Najeriyar ne ya bayyana ba inda ya sake haifar da wannan jinkiri.

‘'To son rai yake cikin kudurin mai yawan gaske don ana son wani sashin kasa ya zama dan bawa ga sauran sasssan, shi yasa mu muka ce bamu yarda ba sai an gyara, don kasa daya al'umma daya dole ne mu amfana da abinda Allah ya azirta kasar nan, wannan shi ya kawo cece kuce. Baya yiwuwa mutumin Akwa Ibom ya amfana amma na jihar Yobe bai amfana ba bayan kuwa za'a je ana kiransu duka ‘yan Najeriya. Wannan a kan haka muka tsaya muka yi wannan gyara kuma ko a yanzu muka dage cewa ba zamu fara ba, sai kowa yaje ya karanta mu gani ko gyaran nan da muka yi shine''.

Akwai fatan cewa dokar za ta kawar da cin hanci

Kodayake bayanai na nuna cewar an yi gyara a kudurin dokar tare da cire dukkanin sassan da suke sanya tada jijiyar wuya, musamman iko ga ministan man fetir da kudin da aka so cirewa al'ummar da ake hakon man da dai sauran batutuwa. Abinda aka sanya a cikin kundin da a yanzu aka rarrabawa ‘yan majalisar domin su yi nazari a kansa amma ga Hon Ahmed Baba Kaita har yanzu fa da sauran rina a kaba a kan wannan kudurin doka.

Nigeria Parlamentspräsident Aminu Tambuwal
Aminu Waziri Tambuwal kakakin majalisar dokokiHoto: picture alliance/Photoshot

‘'Ba zamu yadda cewa a rana daya a je a warware wannan littafin ba, don ya kai shafi 500, abinda muke da matsala das hi shine a warware abin mu san ko menen kafin a amionce das hi, in kuma ba za'a yi haka ba to ba zamu bari ya wuce ba, don ba zamu barai a mayar damu bayi a cikin kasar mu ba. Akwai abinda yake tsorata mu na yaddsa gwamnatin nan mai baring ado take so a yi sauri a kamala wannan kudurin dokar ta PIB, don haka shi yasa muke taka tsan-tsan''.

A yayainda aka sa ido cike da fatar kaiwa ga samun wannan doka da ake hasashen zata sake fasalin tsarin hakowa da ma sarrafa man fetir musamman kawar da cin hanci da rashawa, da kuma hako mai a tafkin Chadi da ke arewacin Najeriya, kaiwa ga hakan a dan lokacin day a ragewa majalisa da bakwa na zama da kaman wuya.