1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Cece-kuce kan shugaban Zimbabuwe

October 22, 2017

An samu martani mabanbanta game da kwace jakadan musamman na Hukumar da Lafiya ta Duniya daga hannun Shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwe.

https://p.dw.com/p/2mK6n
Bildergalerie langjährige Herrscher Robert Mugabe
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Gwamnatim Zimbabuwe ta ce tana girmama matsayin shugaban hukumar lafiya ta duniya bisa matakin karbe mukamun jakadan musamman daga hannun Shugaba Robert Mugabe na kasar ta Zimbabuwe kwanaki kalilan bayan ba shi mukamun na girmamawa. Tun farko bai wa Shugaba Mugabe matsayin na jakadan musamman na hukumar lafiya ta duniya kan chutuka marasa yaduwa ya samu martani na suka a kasashen musamman na Yammacin Duniya.

Tuni babbar jam'iyyar adawa ta MDC da ke Zimbabuwe ta yi maraba da kwace mukamun daga hannun shugaban kasar, saboda abin da ta kira tozarta kasar ta fannin diplomasiyya, dubi da irin iya rashin tafiyar da mulki da ake samu a kasar.

Idan za a iya tunawa ranar Laraba da ta gabata shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana sunan Shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwe a matsayin jakadan musamman na hukumar lamarin da ya cece-kuce.