1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Chadi sun yi afuwa ga 'yan adawa

Abdoulrazak Garba Babani LMJ
November 30, 2021

Wasu 'yan tawaye da 'yan adawa a Chadi, sun shaki iskar 'yanci bayan majalisar sojojin da ke mulkin kasar ta yi musu afuwa.

https://p.dw.com/p/43ffZ
Tschad | Mahamat Idriss Déby, Präsident des Übergangs-Militärrates (CMT)
Shugaban gwamnatin sojojin kasar Chadi, Mahamat Idriss Déby ItnoHoto: Brahim Adji/Tchad Presidential Palace/AFP

Majalisar mulkin sojan kasar Chadin ta dauki wannan matakin ne, domin nuna amincewarta da bukatar kungiyoyin adawa da gwamnatin kasar ta gayyata zuwa taro kan makomar kasar ta Chadi. Majalisar ta ce afuwar za ta shafi wadanda aka yankewa hukunci kan laifukan ta'addanci da zubar da martabar kasa da kuma laifukan da suka shafi bayyana ra'ayi na kashin kai. Sai dai kuma matakin ba ya nufin sakin masu laifin daga gidan yari.

Kungiyoyin 'yan tawayen kasar dai sun ce yin afuwar na daga cikin sharuddan da suka kafa, kafin zama kan teburin tattaunawa da shugaban mulkin sojan kasar Mahamat Idriss Deby Itno wanda ya maye gurbin mahaifinsa da aka kashe a watan Afrilun wannan shekara da muke ciki. Tun dai bayan hawa kan karagar mulkin kasar Mahamat ya rusa majalisar dokokin kasar tare da soke kundin tsarin mulki, inda ya yi alkawarin gudanar da zabe cikin adalci a cikin watannin 18.