1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta rasa mayakanta a wani hari

September 20, 2020

Wasu mahara a yankin tafkin Chadi sun kashe wasu dakarun Chadi a wani sabon hari da aka kai kan mayakan na gwamnati. A nata bangaren gwamnatin kasar ta ce ta kashe maharan.

https://p.dw.com/p/3ilJi
Nigeria Soldaten des Tschad patrouillieren in Monguno
Hoto: AFP/A. Marte

Akalla sojojin Chadi 10 ne suka hallaka wasu bakwai kuwa suka jikkata a wani harin kwantan baunan da ake zargin mayakan Boko Haram da yi wa ayarin dakarun a yankin tafkin Chadi.

Wata majiyar sojan kasar ta tattabar wa kamfanin dillancin larabaran Franasa AFP faruwar lamarin.

Sai dai rundunar tsaron kasar ta Chadi tabbatar da labarin ba, to sai dai ta ce sojojin na kasar sun lalata wani sansanin mayakan kungiyar ta BH a yankin tare da kwasar makamai da dama. 

A cikin watan Afrilun da ya gabata ne dai Chadin ta kaddamar da wani sintirin kakkabe 'yan Boko Haram daga yankin bayan mutuwar sojojin kasar sama da 100, inda kasar ta ce ta kakkashe 'yan bindigar akalla dubu guda daga yankin.