1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Chaina ta saka kudaden fito ga kayayyakin Amirka

Suleiman Babayo
May 13, 2019

Rikicin kasuwanci tsakanin Amirka da Chaina ya janyo kaduwar kasuwar hannun jari a Amirka makonni biyu a jere yayin da Chaina ta mayar da martani kan saka kudaden fito ga kayayyakin da suke fitowa daga Amirka.

https://p.dw.com/p/3IRJD
Symbolbild USA-China-Handelskrieg
Hoto: Colourbox


An samu faduwar kasuwar hannun jari a kasar Amirka a wannan Litinin abin da ke zama makonni biyu a jere ke nan sakamakon cece-kucen kasuwancin da ke wakana tsakanin kasar ta Amirka da kuma Chaina.

Rikicin ya shiga sabon mataki sakamakon martanin da Chaina ta mayar da zai fara aiki a farko watan gobe na Yuni na kakaba kudaden fito ga kayayyakin da za su shiga kasar daga Amirka. Tun farko Shugaba Donald Trump na Amirka ya dankara kudaden fito ga kayayyakin da ke fitowa daga Chaina. Duk bangarorin biyu sun nuna alamun duk da halin da ake ciki za su koma kan teburin tattaunawa ranar Jumma'a mai zuwa.