1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chibok: zanga-zangar zaburar da gwamnati

Yusuf BalaAugust 22, 2016

'Yan fafutikar kwato 'yan matan Chibok sun gudanar da wata zanga zangar da a cikinta suke neman gwamnatin Najeriya ta daina jan kafa tare da daukar matakin da ya dace domin ceto 'yan matan.

https://p.dw.com/p/1JnBG
Nigeria Demonstration Bring Back Our Girls in Chibok
Sama da shekaru biyu kenan daga lokaci zuwa lokaci ake wannan fitowa dan tunatar da gwamnatiHoto: Reuters/A. Akinleye

Kasa da 'yan sa'o'i da fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ke zuwa tarrayar Najeriya, 'yan kungiyar fafutukar ceto 'yan matan Chibok sun gudanar da wata zanga-zangar da a cikinta ke neman gwamnatin kasar ta daina jan kafa tare da daukar matakin da ya dace domin ceto 'yan matan.

Zanga-zangar da ta kunshi wasu a cikin iyayen 'yan matan da kuma 'yan fafutukar da aka gudanar a harabar fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock dai na da zummar sake daukar hankalin mahukuntan kasar da ma kasashe na duniya bisa makomar 'yan matan da ma halin da 'yan gudun hijirar yankin ke ciki a yanzu haka. Abin da ke zuwa tun bayan bayyanar sabon fefen bidiyo da ya nuna yaran cikin wannan wata na Agusta, abin da a yayin zanga-zangar Esther Yakubu da ke zama daya cikin iyayen 'yan matan ke cewa sun gaji da ganin tashin hankali na hotunan 'ya'yansu.