1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta zargi Kirisoci da ayyukan asiri

August 19, 2014

Kiristoci kusandubu ne mahukunta a China suka kama bisa zargin cewa su mambobi ne na kungiyar asiri a cewar rahotannin kafofin yada labarai na kasar.

https://p.dw.com/p/1Cx6w
Christentum China
Hoto: picture-alliance/ROPI

Mahaukuntan Beijing na kasar China sun kame wasu mabiya addinin Kirista kusan dubu tun daga watan Yuni zuwa yau, bisa zargin cewa su mambobi ne na kungiyar asiri kamar yadda rahotannin kafofin yada labarai na cikin gida a kasar suka bayyana.

Wadannan mambobin da suka fito daga kungiyar "Almighty God" a turance da ke samun karin magoya baya daga bangarori daban-daban na kasar na ayyukanta fiye da shekaru goma a wannan kasa ta China.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Xinhua ya ce ba'a fayyace wane laifi ne suka aikata ba, Sai dai ana zarginsu da zama mambobin kungiyar Falun Gon da aka haramta a shekarun 1990. Su kuwa mambobin wannan kungiya sun ce jam'iyyar da ke mulkin kasar ta China mai ra'ayin kwaminisanci na harinsu ne sakamakon barazanar da su ke yi mata na ci gaba da karin samun magoya baya.

Ita dai wannan kasa ta China ta kasance mai ra'ayin juya harkokin da suka shafi addini da ya hadar da rushe wasu kungiyoyi na addinai.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe