1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da kalubalantar shugaban Masar

February 1, 2013

'yan sandan Masar sun yi amfani da karfi wajen hana masu zanga zanga kusantar fadar shugaban kasa a lokacin wata zanga zanga da babbar jam'iyar adawa ta kira a Alkahira.

https://p.dw.com/p/17WpB
Anti-Mursi protesters chant anti-government slogans at Tahrir Square in Cairo February 1, 2013. Opponents of Egyptian President Mohamed Mursi planned mass demonstrations on Friday, raising the prospect of more bloodshed despite a pledge by politicians to back off after the deadliest week of his seven months in office. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)
Kairo Anti Mursi ProtesteHoto: Reuters

Jami'an 'yan sandan Masar sun yi harbe harbe a iska tare da amfani da ruwa mai sa kaikayi, wajen tarwatsa masu zanga-zanga da ke harbinsu da duwatsu a kusa da fadar shugaban kasa a birnin Alkahira. Makamantan wadannan tashe-tashen hankula sun barke a wasu wurare na babban birnin na Masar tsakanin 'yan sanda da kuma masu zanga zanga ciki kuwa har da kusa da ofisoshin jakadancin Amurka da kuma Birtraniya. wadand suka shaidar da lamarin suka ce mutane biyu ne ak garzaya da su asibiti sakamakon raunukan da suka samu.

Dubban mutane ne dai suka fantsama akan titunan birane da dama na Masar ciki har da Port Said domin amsa kirar da babbar jam'iyar adawar Masar ta yi na gudanar da zanga-zanga. Ita dai wannan jam'iya ta na nema ne shugaba Mursi ya kafa gwamnatin hadin kan kasa tare da kwaskware sabon kundin tsarin mulki. Wannan zanga zangar ta gudana ne kwana daya bayan alkawarin da wasu 'yan adawa suka yi na dakatar da tayar da kayar baya da ta lamshe rayukan mutane 56 a cikin mako guda.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi