1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban cin Zarafin mata a Darfur,Sudan

September 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuB9

Kungiyar kare hakkin biladama ta mdd ta bayyana cewa babu alamun wani cigaba adangane da kokarin da akeyi na samar da zaman lafiya a lardin Darfur din kasar sudan.Kommissionar kare hakkin jamaa dake majalisar Louise Arbour,tace bisa ga rahoatannin data samu daga yankin yammacin Sudan din,babu alamun ingantuwan rayuwar alummomi dake wannan yanki da ake fama da rigingimu.Tace ana cigaba da fuskantar matsalolin take hakkokin jama’a,kamar dai yadda aka fuskanta a tun a farkon barkewan wannan rikici a shekara ta 2003.Tace ta samu rahoto dangane da karuwan batutuwan cin zarafin mata ta hanyar yi musu fyade,ba tare da an hukunta wadanda keda alhakin aikata laifin ba.A watan daya gabata nedai kungiyar kare hakkin jama’a ta mdd ta gabatar da rahoto dangane da yadda ake cin zarafin yara mata,alokacin kai hare hare a kauyuka dake Darfur.