1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin 'yan gudun hijira a Jamus

Yusuf BalaSeptember 28, 2014

Jami'an 'yan sandan na Jamus sun kudiri aniyar zurfafa bincike ko za su gano wata aniya ta nuna wariyar launin fata ko kyamar baki kan 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/1DMNK
Polizist Polizei Deutschland Abzeichen Symbolbild
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumar 'yan sanda ta ce ya zama dole a ci gaba da gudanar da bincike kan zargin cewa wasu jami'an tsaro a cibiyar 'yan gudun hijira a yammacin kasar ta Jamus na nuna gallazawa ga 'yan gudun hijirar a fili da boye.

Jami'i mai magana da yawun 'yan sanda ya bayyana a ranar Lahadin nan cewa tuni wasu jamian hukumar 'yan sanda suka dura cibiyar 'yan gudun hijirar ta yankin Burbach dake kusa da birnin Hagen inda suka gudanar da tambayoyi ga jami'an tsaron da 'yan gudun hijira bayan da wani dan jarida ya sami fefen bidiyo da ke nuna yadda wasu jami'an tsaro ke tozarta wani dan gudun hijira.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Ulrich Hanki, ya ce har ila yau hukumar tasu ta sami wani hoto da aka dauka ta hanyar amfani da wayar hannu inda hoton ke nuna wani jami'in tsaro na shurin wuyan dan gudun hijira da aka daure wa hannaye kwance a kasa.

Mista Hanki ya ce wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun fito fili sun bayyana yadda masu lura da su ke gallaza musu, sannan ya ce dukkanin wadannan jami'an tsaro da suka fito daga wani kamfani mai zaman kansa an sallamesu daga cibiyar.

A karshe Hanki, ya ce 'yan sanda da masu gabatar da kara na ci gaba da zurfafa bincike dan gano yiwuwar nuna wariya game da wannan batu.