1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cire Lamido na ci gaba da janyo takaddama

February 21, 2014

A na kara fuskantar fito na fito a game da dakatarwar da Jonathan ya yi wa gwamnan babban bankin kasar, majalisar wakilan kasar ta ce mataki ya saba wa doka.

https://p.dw.com/p/1BDc9
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Ya dai dade da jan daga a tsakaninsa mahukuntan Najeriya bisa tonon sililin da yake yi na batar dabon da makudan kudadde suka yi daga kamfanin man Najeriyar zuwa asusun gwamnatin kasar, abin da ake ganin ya kai ga dakatarwar da aka yi wa gwamnan babban bankin Najeriya.

To sai dai majalisar wakilan Najeriyar ta zama ta farko a hukumance a Najeriyar da ta ja daga da fadar shugaban kasar a game da dakatarwar da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa gwamnan babban bankin Sunusi Lamido Sunusi. Majalisar dai ta dau matsaya kan cewar dakatarwar haramtaciyya ce da ta saba wa dokokin da suka bai wa shugaban Najeriyar ikon nadawa ko tsige ko ma dakatar da gwamnan babban bankin kasar. Ibrahim Tukur El-Sudi ya ce akwai dalilan da suka janyo daukan wannan mataki.

"Wannan dakatarwa bata bisa ka'ida domin idan muka duba sashi na goma sha daya na dokar da ta kafa babban bankin Najeriya, ai baya baiwa shugaban Najeriya ikon cire shi koma dakatar da gwamnan babban bankin kai tsaye ba, har sai an samu kasha biyu bisa uku na ‘yan majualisar datawa. Don haka abinda shugaban kasa ya yi bashi da tasiri kuma ya sabawa doka. Domin wannan ya nuna irin kama karyan da ake yi a kasar nan, ana bincike a majalisa a kan wasu kudade da ake tuhumar ba'a shigar da su a babban bankin Najeriya ba kamar yadda tsarin mulki ya tanada, sai kawai a ce an dakatar da shi? Ya dace a kamala binciken."

Sanusi Lamido Sanusi Gouverneur Zentralbank Nigeria
Hoto: Reuters

Wannan dai na nuna irin cece kucen da ke kara kaurewa a game da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka da tuni ya sanya jan daga a tsakanin al'ummar kasar da wasu ke hangen an saba doka.

Tuni kungiyoyi da ke fafutukar yaki da cin hanci da rashawa suka ce matakin yunkuri ne na tsuke bakin masu tona asirin masu halin bera da suka addabi dukiyar Najeriya, kuma yana da mumunar illa ga yaki da cin hancin kasa, kamar yadda Auwal Musa Rafsanjani na gamayyar kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa ya bayyana.

"Mun fuskanci cewa gwamnati tana ci gaba da toshe bakin wadanda suke tona asirin cin hanci da rashawa a Najeriya, misali akwai wani shugaban sashin hana cin hanci a kamfanin mai na NNPC, saboda ya hana cin hanci aka kashe shi wajen shekaru uku ke nan, kuma ba abin da ya faru, sannan yanzu ga na gwamnan babban bankin Najeriya Sunusi Lamido Sunusi, saboda ya tona asirin irin cin hanci da ake yi a kamfanin albarkatun man fetir shima an dakatar da shi. To wannan ya nuna mana cewa shugaban Najeriya ba ya son ganin an daina cin hanci da rashawa a kasar."

Zentralbank von Nigeria

A yayin da lamarin ke kara zafafa a Najeriyar, da alamun gwamnatin kasar ta yi amai ta lashe bisa cewar babu cin fuska, bita da kulli ko muzgunawar da za ta yi wa Sanusi Lamido Sunusi, domin da saukarsa Najeriya ya hadu da fushin jami'an hukumar tsaro ta farin kaya da suka yi awan gaba da takardun tafiyar na passport.

Wannan lamari na kara zafafa a kasar domin tuni wasu gwamnonin jam'iyyar adawa ta APC na Kano da Lagos suka yi watsi da matakin da shugaban Najeriyar ya dauka na dakatar da gwamnan babban bankin kasar, yayain da tsohon matakimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya ce kamata ya yi ya nufi kotu kawai domin shima an taba yi masa haka kuma ya nemi 'yancinsa a gaban kuliya.

Duk da cewa Sunusi Lamido Sunusi ya fito fili ya ce baya son karin wa'adin mulki a matsayinsa na gwamnan babban bankin Najeriya, amma a bayyana take cewa za'a fafata da shi a kan wannan lamari da ke daukan hankali jama'a a yanzu.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar