1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CLEMENT YA GABATAD DA RAHOTONSA KAN HALIN TATTALIN ARZIKIN JAMUS

Yahaya AhmedJanuary 26, 2005

Ministan tattalin arzikin tarayya, Wolfgang Clement, ya sami goyon bayan majalisar ministoci game da rahoton halin tattalin arzikin Jamus da ya gabatar a fadar gwamnati da ke birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/BvdR
Ministan tattalin arzikin Jamus, Wolfgang Clement
Ministan tattalin arzikin Jamus, Wolfgang ClementHoto: AP

Bisa kiyasin da ministan tattalin arziki na tarayya, Wolfgang Clement ya yi, wanda kuma gwamnatin tarayya ta amince da shi dai, za a sami bunkasar tattalin arziki na kashi daya da digo 5 zuwa kashi 2 cikin dari a wannan shekarar. Hakan kuwa, abin faranta rai ne inji ministan, saboda alkaluman da aka samu na nuna cewa, hada-hadar cinikayya da na kasuwanci a nan cikin gida Jamus, ita ma za ta bunkasa:-

"Tattalin arzikin Jamus ta fara bunkasa. Yanzu abin da ake bukata ne, aiwatad da kudurorin da aka riga aka zartar – alal misali a kasuwar kwadago, don a ci gaba da iskar da ke kadawa ta farfaddo da tattalin arziki har a kai ga samun bunkasa mai dorewa."

Ministan dai ya bayyana manufarsa dalla-dalla. Ba ya son jin koke-koken da wasu bangarori ke yi game da kwaskwarimar da gwamnati ta gabatar, mai gurin hanzarta farfadowar tattalin arzikin kasar baki daya. A jerin kafofin da aka yi musu kwaskwarimar, kasuwar kwadago ce kan gaba, inda aka fi mai da hankali wajen rage yawan matasa marasa aikin yi. Sai kuma yunkurin da ake yi na ganin cewa, kafofin kula da inshwarar lafiya, da harkokin fansho, da dai sauransu sun zaunu sosai, duk da matakan tsimin da gwamnati ta dauka, wadanda ke shafan kudaden shigar jama’a. Game da wannan batun dai, ministan ya bayyana cewa:-

"Gurin da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba a lokaci matsakaici shi ne, rage kudaden da ake kashewa kan albashi da kashi 40 cikin dari. A cikin yanayi kamar nan Jamus, inda ake bin tafarkin jari hujja, ba za a iya ci gaba da dogara kan gwamnati kacokan, wajen biyan duk kudaden kiwon lafiya, da na fansho da na marasa aikin yi ba, musamman ma Idan aka yi la’akari da tsarin al’umma halin yanzu. Ci gaba da tallafin gwamnati a wadannan fannonin kamar a da, zai janyo gagarumin cikas ga manufofin tattalin arzikinmu gaba daya."

A halin yanzu dai, ana kashe kusan rabin kasafin kudin gwamnatin tarayya ne, a fannonin kiwon lafiya, da fansho da dai sauransu. Har ila yau dai, kwaskwarimar da aka yi da nufin rage yawan kudaden da ake kashewa, ba ta fara nuna alamun wani sakamako ba tukuna. Amma gwamnati na kyautata zaton cewa, daga cikin watan Maris ne za a dinga ganin fa’idar da matakin zai jawo. Ministan tattalin arziki Wolfgang Clement, ya musanta zargin da ake yi wa gwamnatin na cewa, ta gaza rage yawan marasa aikin yi a kasuwar kwadago. A ganinsa dai, alkaluman da Hukumar kwadago za ta buga na yawan marasa aikin yi a cikin wannan watan na Janairu, ba za su sami wani angizo, kan sakamakon da ake sa ran samu a cikin watan Maris din ba. Sai dai ya kuma ce, ba zai iya karyata rahotannin da ke nuna cewa yawan marasa aikin yin zai wuce miliyan 5 a cikin watan Janairun ba.

Bisa rahoton da ministan ya gabatar dai, yawan marasa aikin yin zai tsaya ne a miliyan 4 da digo 53.

A daya bangaren kuma, masana tattalin arziki da dama sun nuna shakkunsu kan alkaluman da gwamnatin ta gabatar. kungiyar masana’antun Jamus ta ce, a nata kiyasin, ba za a sami bunkasa fiye da kashi daya da digo 5 cikin dari a wannan shekarar ba. Jam’iyyun adawa ma, ba su yi wata-wata ba, wajen yi wa rahoton gwamnatin kakkausar suka. A nasu ganin dai, rahoton ba ya kunshe da kome, illa yabon kanta da gwamnatin ke yi.