1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Duniya cikin alhini

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 26, 2020

Al'ummar duniya na ci gaba da zama cikin firgici dangane da annobar cutar Coronavirus, duk da cewa ana warkewa.

https://p.dw.com/p/3a5ys
Taiwan Taipei | Übung gegen Ausbreitung des Coronavirus (picture alliance/AP Images)
Har yanzu ana laluben maganin CoronavirusHoto: picture-alliance/AP Images/Yomiuri Shimbun

Da fari dai cutar ta Coronavirus ko kuma COVID-19, ta bulla ne a kasar Chaina, kafin daga bisani sannu a hankali ta mamaye duniya baki daya. An yi gargadin cewa idan ba a dauki matakan kariya cikin gaggawa ba, cutar za ta yi gagarumar illa a duniya baki daya, ganin cewa har kawo yanzu ba ta da magani.

Wanna dai ya sanya firgici cikin zukatan al'umma, musamman a kasashe masu tasowa, da suke fama da dinbim talauci da halin rashin tabbas musamman a bangaren kiwon lafiya. Kasashen Afirka na daga cikin kasashen da ke fama da talauci da matsala a fannin kula da lafiyar al'umma, kuma kawo yanzu kasashe kalilan ne cutar ba ta isa ba a nahiyar.

Kawo yanzu dai cutar ta halaka mutane sama da dubu 22 a fadin duniya baki daya, yayin da wasu dubbai ke kwance a asibitoci suna fama, baya ga wasu masu tarin yawa da suka warke daga cutar.