1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cote D'ivoire za ta yi wa Simone Gbagbo shari'a a kasar

September 20, 2013

Kasar Cote D'ivoire ta ce za ta yi wa Simone Gbagbo shari'a a cikin kasar maimakon aikewa da ita kotun ICC da ke Holland inda ake nemanta ruwa a jallo.

https://p.dw.com/p/19lNZ
Hoto: Getty Images

Mahukuntan Cote D'ivoire sun ce ba za su tasa keyar Simone Gbagbo, uwargidan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo zuwa kotun hukuntan laifukan yaki ta kasa da kasa da ke birnin Hague na kasar Holland ba, don yi mata shari'a bisa zargin aikata laifukan yaki.

Gwamnatin ta Cote D'ivoire ta yanke wannan hukunci ne bayan da majalisar ministocinta ta kammala wani taro a wannan Juma'ar, inda ta ce ta zabi ta yi mata shari'a a kasar kasancewar an daidaita al'amuran shari'a wanda zai taimaka wajen yi mata adalci, hasali ma laifukan da ake tuhumarta da aikatawa ta yi su ne cikin kasar.

Wannan dai na zuwa daidai lokacin da 'yan Afrika ke cigaba da adawa da kotun saboda a cewarsu kotu tai maida hankalinta ne kawai ga yi wa shugabannin Afirka shari'a, na baya-bayanan nan shi ne mataimakin shugaban Kenya William Ruto wanda aka fara shari'arsa a kwanakin baya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman