1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cote d'Ivoire:Hukuncin dauri rai ga sojoji

Gazali Abdou Tasawa
April 11, 2017

A kasar Cote d'Ivoire wata kotun birnin Abijan ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu sojojin kasar guda biyar da ta samu da laifin kisan wasu mutane hudu da suka hada da Faransawa biyu a 2011

https://p.dw.com/p/2b53G
Elfenbeinküste Bürgerkrieg
Hoto: imago stock&people

A kasar Cote d'Ivoire wata kotun birnin Abijan ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu sojojin kasar guda biyar da ta samu da laifin kisan wasu mutane hudu da suka hada da Faransawa biyu bayan da suka sato su daga Otel din Novotel ta birnin na Abijan a shekara ta 2011. 

Daga cikin sojojin 10 da kotun ta samu da hannu a cikin aikata wannan laifi da hukuncin ya shafa har da Janar Brunot Dogbo tsohon babban kwamandan na rundunar sojin gandroba ta kasar. 

A ranar hudu ga watan Aprilun shekara ta 2011 ne a tsakiyar rikicin bayan zaben da ya kai ga kame Shugaba Luarent Gbagbo, sojojin suka kutsa a cikin Otel Novotel ta birnin Abija inda suka yi awon gaba da daraktanOtel din Stephane Frantz Di Reppel da Yves Lambelin babban daraktan kamfanin sarrafa kayan gona na Sifka dukkaninsu 'yan Faransa da wasu ma'aikatan kamfanin na Sifco su biyu daya dan kasar Benin daya kuma dan Malesiya inda suka kaisu a fadar Shugaban kasa suka gana musu azaba har mutuwa, kana suka jefa gawarwakin a cikin teku.