1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda suka mutu da coronavirus sun karu

Abdoulaye Mamane Amadou
May 22, 2020

Adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a duniya sun haura miliyan biyar, a yayin da fiye da mutun 329.790 suka gamu da ajalinsu biyo bayan sun kamu da annobar Covid-19.

https://p.dw.com/p/3cbOR
Coronavirus | Brasilien Manaus Beisetzung von Opfern auf Friedhof
Hoto: Imago Images/Fotoarena/S. Pereira

An lura da samun karuwar mutuwar jama'ar da suka kamu da cutar a baya bayan nan a yankin Latin Amirka, inda a kasar Brazil kawai mamata suka zarta fiye da mutun dubu 20 000 da suka mutu da cutar. Har yanzu Amirka ita ce ke kan gaba daga cikin jerin kasashen da cutar ta yi wa mummunar barna, inda take da mamata 94.661. Birtaniya na da mamata 36.042. Italiya 32.486.  Faransa 28.215, sai Spain 27.940. Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce yana sanya takunkumin fuska lokaci zuwa lokaci idan har bukatar hakan ta taso, to amma sai dai yana guje sanyashi a gaban 'yan jarida, sai kalamun shuigaban na zuwa ne a daidai lokacin da ya bayar da umarnin sasauto tutocin kasar domin nuna jimami ga wadanda suka rasa ransu da cutar ta corona a kasar.