1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta yi watsi da maganin COVID-19

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 3, 2020

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa maganin cutar COVID-19 da Madagaska ta ba ta, ba komai ba ne illa sinadarin maganin zazzabin cizon sauro, a dangane da haka ba za ta yi aiki da shi ba.

https://p.dw.com/p/3elOJ
Guinea-Bissau Coronavirus Tee aus Madagaskar
Maganin coronavirus daga kasar MadagaskaHoto: DW/B. Darame

Najeriyar dai ta dauki lokaci mai tsawo tana bincike a kan maganin da kasar Madagaskar ta bai wa kasar kyauta domin shawo kan cutar sarkewar numfashin ta COVID-19, inda bayan bincike na kimiyya aka fitar da sakamako na sinadaran da ke cikin magani da aka ce yana cike na sinadarai na Tazargade. Tun a ranar 16 ga watan Mayun wannan shekarar ne dai, Najeriya ta karbi maganin cutar coronavirus din daga kasar Madagaskar, inda kuma nan take shugaban kasar ya yi alakwarin za a gudanar da bincike na kimiyya.

Tuni dai 'yan Najeriyar da suka sa ran samun sauki ta hanyar kokarin da ake ganin Madagaskar ta yi, suka fara mayar da martani a kan sakamakon binciken kimiyyar da aka gudanar din. A yanzu dai  kallo ya sake komawa sama musamman ga kasashen Afirka, na su jajirce domin nemo maganin COVID-19 din, ba wai zura idanu na zaman tsammanin samun mafita daga kasashen da suka ci gaba ba, duk kuwa da cewa  fiye da rabin wadanda suka kamu da cutar a Afrika sun warke.