1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Cholera ta bullo a jihar Filato

October 24, 2013

Hukumomin kiwon lafiya a jihohin Filato da Nasarawa suna kan kokarin shawo kan cutar amai da gudawa da ta barke a garin Namu, dake kan iyakar jihohin biyu.

https://p.dw.com/p/1A5kJ
Hoto: DW

Hukumomin kula da lafiya a jihohin Filato da Nasarawa suna kan kokarin shawo kan cutar Ammai da gudawa data barke a garin Namu, dake kan iyakar jihohin biyu.

Ya zuwa yanzu dai marasa lafiya da wannan cutar ta shafa suna kwance a cibiyoyin kiwon lafiya dake garin, inda suke karban jiyya. Na zanta da wasu daga cikin su, inda suka bayyana min hali da suke ciki,inda suka ce suna zaune ne kawai sai suka soma jin sauyi a jiki, inda nan take sai suka soma jin bayan gida, da ammai, kuma babu wani abincin da suka ci daya janyo musu wannan cuta a cewar su.

Binciken da na gudanar ya nuna cewar tun ranar 7 ga wannan wata ne aka soma ganin alamun cutar, tsakanin wadanda suke zaman neman mafaka, tare da yan'uwa da dangogi bayan tashin hankalin daya auku kwanan baya a garin Assakio cikin jihar Nassarawa.

Na zanta da dangogin wasunsu dake kwance a asibitin garin Namu, inda suka yi karin bayani game da alamomin cutar.

"Suka ce sun soma ganin alamun ruwa na fita daga bakin su, wasun su kuma suna bayan gida babu adadi, don haka suka garzaya dasu Asibiti, inda aka kwantar dasu ana basu kulawa “

Akasari dai mata ne da yara tare da tsofaffi wannan cuta tafi shafa, inda wata majiya tace dani akwai akalla mutane 20 da cutar ta kashe, to sai dai hukumomin lafiya a Filato suka ce suna kan bincike don gano ko wace irin cuta ce domin babu tabbas kan cewar cutar Kolera ce, kuma ma, mutane 9 ne suka tabbatar da mutuwar su. Dr. Reymond Juryit, babban jami'i ne a maikatar lafiya ta jihar Filato.

“ Yace sun dauki alamun bayan gida da sukayi gwaji amma basu tabbatar da cewar cutar Kolera ce ba tunda basu gama bincike kan cutar ba. “

To a halin yanzu dai hukumomin Filato da Nasarawa sun dukufa kan aikin bada magani, tare da shelar tsaftar muhalli a garin Namu, don gudun bazuwar cutar zuwa wasu yankuna kamar yadda Alhaji Alhassan Barde, babban jami'in hukumar agaji ta SEMA ya shaida min.

Die Last auf den Schultern der neuen Regierung - Nigeria vor der Wahl Flash-Galerie
Cutar cholera sakamakon rashin ruwa mai tsabtaHoto: DW/Stefanie Duckstein

“Yace sun rigaya sun kai magunguna tare da maikatan kiwon lafiya zuwa yankin da abin ya bulla, kana gwamnatin jihar nasarawa ta aike da nata gudummawar. “

A dai dai lokacin hada wannan rahoto na tarar da manyan jami'ai daga hukumar samar da ruwa mai tsafta a jihar Filato karkashin jagorancin Mrs. Hannatu Dangtong, suna aikin duba rijiyoyoin burtsatse dake garin Namu, don tabbatar da ganin an samar musu da tsafttacen ruwan sha da zummar kawar da wannan cuta ta amai da gudawa dake neman lakume rayukan jama'a.

Mawaallafi: Abdullahi Maidawa Kurgwi
Edita: Umaru Aliyu


Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani