1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola ta bulla a kasar Senegal

August 29, 2014

Hukumomi a kasar Senegal sun bayyana cewar an samu bullar cutar nan ta Ebola a karon a kasar wadda ke yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1D3j4
03.09.2014 DW fit und gesund Ebola Virus
Hoto: Fotolia

Ministan kiwon lafiyar kasar ta Senegal Awa Marie Coll Seck shi ne ya tabbatar da hakan a wani jawabi da ya yi ga manema labarai dazu inda ya ke cewar wanda ya kamu din wani matashi ne da ya koma kasar daga Gini.

Bullar cutar a Senegal dai na zuwa bayan da Kungiyar Lafiya ta Duniya ta ce yawan wadanda suka kamu da cutar a yammacin Afirka a makon da ya gabata shi ne mafi muni tun bayan da cutar ta bayyana a yankin.

A wani karin haske da ta yi dazu, kungiyar ta ce mutane sama da dari biyar ne suka kamu a makon da ya gabata kadai kuma galibinsu a kasar Liberiya ne ko da dai ta ce an samu karuwar masu dauke da cutar a kasashen Gini da Saliyo.

Kimanin mutane 1500 ne yanzu haka aka bada labarin rasuwarsu tun bayan da cutar ta bayyana a Afirka ta yamma kuma a jiya Alhamis Kungiyar Lafiyar ta Duniya ta ce alamu na nuna cewa mutane dubu 20 na iya kamu da cutar kafin a kai ga shawo kanta duba da yadda ta ke bazuwa cikin sauri.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman