1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola ta sake bullowa a Kasar Guinea

Kamaluddeen SaniMarch 18, 2016

Gwamnatin kasar Guinea ta bayyana sanarwar bullar cutar Ebola a jikin wasu mutane biyu da wani gwaji yayi nuni da cewar suna dauke da cutar, bayan da kasar ta ayyana nasarar kakkabe cutar a watanin da suka gabata.

https://p.dw.com/p/1IFq7
Symbolbild Guinea Ebola
Hoto: picture-alliance/dpa/Cabinet Minister De Croo

Kakakin mai Magana da yawun hukumar yaki da cutar a kasar Ibrahima Syalla ya fada a ranar alhamis din nan cewar, cutar ta kunno kai ne daga gidan wasu iyalai a Koropara da ke da nisan kilomita dubu daya da Conakry babban birnin kasar, a inda ya kara da cewar a kwai yiwuwar Karin samun mutane uku masu dauke da kwayar cutar ta Ebolan.

Kazalika Ibrahima Syalla ya ce tuni hukumomin lafiyar kasar Guinean suka fara daukar matakan dakile bazuwar cutar zuwa wasu yankunan kasar.

Hukumomin da ke yaki da cutar hade da ministan harkokin lafiyar tuni suka kira wani taron gaggawa domin duba yadda zasu tinkarin yadda za a dakile cutar da yanzu haka ke barazana ga al'ummar kasar.