1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da alamun Cote D´Ivoire ta kama hanyar samar da zaman lahia

June 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buvi

A game da Cote d´Ivoire ɗin, bisa dukkan alamu ƙasar ta kama turbar samar da zaman lahia.

An gano wannan alamomi, a sakamakon yini 2, da ya haɗa tawagogin rundunar gwamnati ,da ta yan tawaye, a birnin Yamouscouro.

Ɓangarorin 2, sun jaddada bukatar su, ta fara kwace makamai, da kuma rijistar mutane, a shirye shiryen zaɓɓukan da za a gudanar kamin ƙarshen watan oktber mai zuwa.

Sanarwar ƙarshen taron da su ka rattaba hannu kanta,ta tanadi ranar 8 ga watan da mu ke ciki, a matsayin ranar fara kwance ɗamara.

A matakin farko, rundunonin 2, za su tattara dakarun su, a wassu sansanoni na mussamman, bisa sa idon dakarun shiga tsakani na Majalisar Ɗinkin Dunia, da na ƙasar France.

A wani jawabi da shugaban ƙasa Lauran Bagbo ya yayi, ta kafofin sadarwar, ya jinjina damtse, ga praministan riƙwan ƙwarya, Charles Konnan Banny, a game da ƙoƙarin da ya ke, na maido da kwanciyar hankali a wannan ƙasa.