1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Beljiyam: Dalibai na fafutukar kare muhalli

Yusuf Bala Nayaya
February 14, 2019

Dubban yara 'yan makaranta ne a Beljiyam suka kaurace wa makarantu don shiga zanga-zangar neman kawo sauyin gwamnati a harkokin da suka shafi tunkarar batutuwa na sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/3DO4m
Belgien Brüssel Demonstration gegen Klimawandel
Hoto: Reuters/F. Walschaerts

A wannan Alhamis cikin wadanda suka fita gangamin har da dalibai na jami'a da tsofaffin mutane wadanda ke neman kari na matsin lamba ga mahukunta ta yadda za su kara azama a aikin da suke yi don alkinta muhalli da kauce wa dumamar yanayi.

'Yan sanda sun bayyana cewa gangamin da aka yi a birnin Brussels a wannan rana ta Alhamis ya samu mahalarta kimanin 11,000.

Daliban da dama dai sun fita gangamin da ake fita duk Alhamis makonni shida ajere duk kuwa da yadda malamai ke neman sanyaya gwiwar daliban kada su bar ajin karatunsu.

An dai faro gangamin da wasu mutane dubbai da sannu a hankali suka kai 35,000 a makonni biyu da suka gabata. Babban burin gangamin dai shi ne matsin lamba gabanin zabukan da za a yi a mataki na kasa da ma Kungiyar Tarayyar Turai.