1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daliban jami'ar Jos sun yi zanga-zanga

Ahmed SalisuNovember 24, 2014

Rahotanni daga birnin Jos na jihar Filato a arewacin Najeriya na cewar daliban jami'ar a birnin sun gudanar da wani bore da ya yi kokarin rikidewa zuwa tashin hankali.

https://p.dw.com/p/1DsOT
Symbolbild Gewalt in Nigeria
Hoto: SEYLLOU DIALLO/AFP/Getty Images

Wakilinmu da ke birnin Abdullahi Maidawa Kurgwi ya ce daliban sun yi boren ne saboda karin kudin makaranta da suka ce hukumomin jami'ar Jos sun yi wanda suka ce ya fi karfin iyayensu.

Yayin boren dai an lalata wasu gine ginen jami'ar, kana daliban sun rufe wasu manyan hanyoyin shiga birnin Jos har na tsawon lakaci kafin daga bisani jami'an tsaro su shiga tsakani don kwantar da kurar.

Cikin zantawarsu da wakilinmu, mataimakin shugaban jami'ar ta Jos, Parfessa Hayward Babale Mafuyai ya ce sun soke batun karin kudin kuma an kafa kwamitin da zai sassanta da daliban.