1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalilin fitar da gumi daga jikin dan Adam

Aliyu AbdullahiSeptember 3, 2015

Dalilan da suke saka gumi ke fita daga jikin mutum yayin da ya sha ko yake shan ruwa, musamman ma a irin wannan lokacin na zafi.

https://p.dw.com/p/1GQYP
Pakistan Hitzewelle
Hoto: Reuters/A. Soomro

Maganar dai gumi a jikin mutum yana da mahimmanci kwarai da gaske, ko ya sha ruwan zafi ko bai sha ba, domin idan mutum ya sha ruwan zafi jikinsa zai yi dum... za ka ga zufa ya keto masha a jiki. Wannan yana daya daga cikin hanyoyin da jikin bil 'adama ke amfani da su wajen ganin cewa zafin jikin mutum (wanda ake kira temperature), bai wuce ma'aunin celcius 37 ba, wanda idan ya kai 38, ko 39 har zuwa 40 to an shiga yanayi na matsala dan ana iya rasa rai. Har ila yau, idan zafin ya yi kasa da ma'aunin celcius 32 anan ma, mutum yana iya rasa ransa. Dan haka dan jikin mutum yayi amfani sosai na'urorin jikinshi suyi amfani da sauransu, jikin baya son zafin ya wuce wannan sikelin na celcius na 37.

To idan zafin jikin mutum ya hau, wannan hanya na fitar da gumi na daya daga cikin hanyoyin warware matsalar. A jikin dan adam akwai wasu halittu da ake kira da Turanci (sweat glands) wato wasu daruruwan kananan kofofin gashi ne a fatar jikin bil adama, wadanda aikinsu kawai su fitar da gumi daga jikin dan adam a lokacin da ya dace ba dan komai ba, sai dan zafin jikin dan adam ya sauka. Kuma idan ka duba yanayin halittar dan adam, ba sai ya sha ruwa ba kawai zai yi gumi, yin aikin karfi da sauransu za ka ga ya jike jakab da gumi, haka idan kaci abinci mai zafi, sau da yawa sai ka hada da fifita dan za ka ji gumi ya kwararo maka nan take. A wasu lokutan ma, mutum sai ya saka jubga-jubgan kayan sanyi a jika, gashi kuma ba sanyi ake yi ba, dole kayi gumi, ko kuma ka zauna a guraren kira ko wani kamfanin da ake aiki da wuta ko gashi haka, dole ne aji gumu ya keto.